Philippians 3

Ban da Dogara a Jiki

1A ƙarshe, ʼyanʼuwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne.

2Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki. 3Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba, 4ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka.

In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi:
5an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Israʼila ne, na kabilar Benyamin, Baʼibrane ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne; 6wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga tafarkin doka, ni marar laifi ne.

7Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. 8Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi 9a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi-adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya. 10Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamarsa a cikin mutuwarsa, 11yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.

Nacewa Zuwa ga Manufar

12Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi. 13ʼYanʼuwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi: Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba, 14ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.

15Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma. 16Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.

17Ku haɗa kai da waɗansu cikin bin gurbina, ku kuma lura da waɗanda suke rayuwa bisa ga ƙaʼidar da muka ba ku. 18Gama kamar yadda na sha gaya muku yanzu kuma ina sāke gaya muku har ma da hawaye, waɗansu da yawa suna rayuwa kamar abokan gāban gicciyen Kiristi. 19Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya. 20Amma mu ʼyan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, 21shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yǎ mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

Copyright information for HauSRK